Shugaban kamfe din Peter Obi ya ajiye mukaminsa

Doyin Okupe 1
Doyin Okupe 1

Darekta Janar na yakin neman zaben Peter Obi a matsayin shugaban Najeriya karkashe inuwar jam’iyyar LP, Doyin Okupe ya sauka daga mukaminsa.

Ya sanar da haka ne a wata wasika da ya aike wa Obi a ranar 20 ga watan Disambar, 2022.

A cewarsa, ya sauka ne saboda kada abubuwan da ke faruwa da shi su shafi yakin neman zaben Peter Obi a 2023.

Murabus din Doyin Okupe na zuwa ne kwana guda bayan da kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari saboda laifin rashawa.

Tun a shekarar 2019 ne hukumar EFCC ta gurfanar da Mista Okupe a gaban kotu kan zargin karɓar kuɗaɗe daga ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro, waɗanda ya gaza yin bayani kansu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here