An rantsar da shugaba mafi dadewa a duniya karo na shida

FB IMG 16705870717761443
FB IMG 16705870717761443

An rantsar da shugaban ƙasar Equatorial Guinea, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo karo na shida a kan karagar mulki.

Shugaban mai shekara 80, ya kasance shugaban kasa mafi dadewa a duniya.

Ya yi alkawarin tafiya da kowa a ƙasar, inda ya ce zai zama shugaba ga kowa. Ya fara hawa kan mulki ne a shekara ta 1979 bayan wani juyin mulki da ya jagoranta.

Masu suka dai sun ce tun bayan lokaci da ya karbi mulki ake ta tafka a magudi a kowane zabe da aka gudanar, inda ake hana ‘yan adawa shiga zabuka da kuma tilastawa kafafen ƴada labarai yin abin da gwamnati da kawayenta ke so

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here