Mahaifiyar Dan takarar gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar NNPP Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ta rasu tana da shekaru 88 a Duniya.
Hajiya Rabi Abdullahi, ta rasu ne a ranar Asabar 5 ga watan Nuwambar 2022, bayan fama da gajeriyar jinya.
Mai magana da yawun Abba Kabir Yusuf Dan takarar gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar NNPP, Sunusi Bature Dawakin Tofa, shi ne ya sanar da rasuwar ta cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Kano.
Ta cikin sanawar Dan takarar gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya mika sakon ta’aziyyarsa, Inda ya yi fatan Allah ubangiji ya rahamceta, yasa Aljanna ce makomar ta.
Kazalika Dawakin Tofa, yace za a yi janaizar ta da misalin Karfe 4 na yammacin ranar Asabar 5 ga watan Nuwambar Shekarar 2022, a Masallacin Al-Furqan dake Alu Avenue a Nasarawa GRA.
Hajiya Rabi, dai ta rasu ta bar ‘Ya ‘Ya 2 da jikoki 48, da sauran ‘Yan uwa da dama.













































