APC ta bukaci hukumar zabe ta sanya Machina a matsayin Dan takatar Sanatan Yobe ta arewa

Bashir Machina and Ahmad Lawan
Bashir Machina and Ahmad Lawan

Jam’iyya mai mulki ta kasa APC a hukuman ce ta rubutawa hukumar zabe mai zaman kanta wasika kan amincewa da Bashir Machina a matsayin dan takarar sanatan Yobe ta Arewa kamar yadda babbar kotun tarayya da ke Damaturu ta bayar.

Takardar wadda ta samu sa hannun shugaban jam’iyyar na kasa Abdullahi Adamu da Sakatare Sanata Iyiola Omisore.

Jam’iyyar a cikin wasikar ta umurci hukumar zaben da ta buga sunan Machina kamar yadda kotu ta bayar.

“Muna mai sanar da hukumar zabe mai kwanan wata 28 ga Satumba 2022, da kuma oda mai kwanan wata 5 gawatan Oktoba 2022, daga babbar kotun tarayya da ke Damaturu, inda muke umartar hukumar ta amince da Machina a matsayin dan takarar jam’iyyar na Sanatan Yobe ta Arewa.

Idan za a iya tunawa, wata babbar kotun tarayya da ke Damaturu ta yanke hukuncin cewa shugaban majalisar dattawan Najeriya Ahmad Lawan, ba ahi ne sahihin dan takarar jam’iyyar APC na Yobe ta Arewa ba ne a zaben 2023 me zuwa.

Daga nan ne kotun ta tabbatar da Machina a matsayin dan takarar jam’iyyar, bayan da ya lashe zaben fidda gwani da aka amince da shi bisa ka’ida, wanda hukumar zaben ta sa ido yayin aiwatar da shi.

Machina ya shigar da kara yana rokon kotu ta yanke hukuncin cewa shi ne dan takarar jam’iyyar. Ya kuma roki kotun da ta umurci hukumar zabe INEC da ta saka sunansa a cikin rajista ta karshe na ‘yan takarar zaben majalisar dokoki ta kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here