Yan ta’adda sun sako sauran mutane 23 da harin jirgin kasan Abuja-Kaduna ya rutsa da su

Abuja Kaduna Train Attack Victims 1 1
Abuja Kaduna Train Attack Victims 1 1

Gwamnatin tarayya ta ce an sako dukkan fasinjojin da aka yi garkuwa da su daga jirgin kasa da yawo daga Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga Maris 2022.

Shugaban Kwamitin ayyukan tsaro Farfesa Usman Yusuf ne ya sanar da hakan a ganawar sa da manema labarai a yammacin yau Laraba.

“Ina mai farin cikin sanar da al’umma da duniya baki daya cewa da karfe 4 na yammaci 5 gawatan 10 2022, kwamitin mutane bakwai na shugaban kasa karkashin babban hafsan hafsoshin sojoji Janar Leo Irabor ya tattara, ya tabbatar da sakin sauran fasinjoji 23 da akayi garkuwa da su wadanda ‘yan ta’addar Boko Haram suka kai hari kan jirgin kasan fasinjojin Abuja zuwa Kaduna a ranar 28-3-2022.

“Al’ummar kasa na bin bashin godiya ga Sojojin Najeriya karkashin jagorancin babbar tawaga wadanda suka dauki ga6aren tunkarar aikin daga farko har karshe.

“Dukkannin Hukumomin tsaro da ma’aikatar Sufuri ta tarayya sun ba da gudummawa matuka sosai dan ganin an samu nasara a wannan aiki.

“Tallafin da shugaban kasa kuma kwamandan askarawan sojin Najeriya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ke bayarwa shi ne ya sanya hakan ta wakana ayau.

“Mambobin wannan kwamiti suna godiya da irin jajircewa da hadin kai da aka ba su na kasancewa cikin wannan aiki. Allah madaukakin sarki ya tabbatar mana da hadin kai, ya kuma kawo mana zaman lafiya a kasarmu.”

Idan za a iya tunawa a ranar 28 ga watan Maris ne ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane suka kai hari kan wani jirgin kasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna, inda suka kashe mutane kusan takwas tare da yin awon gaba da fasinjoji sama da 60.

Tuni dai gwamnatin tarayya ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna tare da yin alkawarin saukaka wa duk wanda aka kama.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here