Hukumar kulada da aikin ‘yan sanda ta kasa ta kori wasu manyan jami’an ‘yan sanda bakwai bisa rashin da’a tateda rage ma wasu jami’ai goma karin girma.
Kakakin hukumar Ikechukwu Ani ne yabbana haka lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja, ya ce an dauki matakin ne a cigaba da babbab taro da hukumar keyi karo na 15.
Mista Ani ya ce taron wanda mukaddashin shugaban hukumar Mai shari’a Clara Ogunbiyi ta jagoranta tace anyi la’akari da al’amuran ladabtarwa da ke kunshe cikin hukumar.
Ya ce, jami’an da aka kora sun hada da mukamin CSP 1, SP 1 da kuma ASP 5.
Hukumar ta kuma rage wa jami’an masu mukamin ASP 4 daraja zuwa Sufeto, yayin da aka ja kunnen manyan jami’an ‘yan sanda 10 da suka hada da ACP, CSP, SP da DSP 2.
Rahotanni sun ce mai shari’a Ogunbiyi yace daga yanzu hukumar za ta ba da kulawar ta musamman domin a hukunta wadanda aka samu da laifi nan take.
A cewar Mai shari’a Ogunbiyi ya yi kira ga jami’an ‘yan sanda da su tabbatar da cewa suna gudanar da aiki bisa ka’idojin da aka kafa tare da kaucewa daukar doka a hannunsu.











































