Buhari ya yi maraba da sako sauran mutanen da harin jirgin kasa ya rutsa da su

Muhammadu Buhari 1
Muhammadu Buhari 1

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana farin cikinsa da jin dadinsa da yadda sojoji da sauran jami’an tsaro sukayi na sako sauran fasinjojin jirgin kasa 23 da aka yi garkuwa cikin koshin lafiya.

Fasinjojin da abin ya shafa dai ‘yan ta’addar Boko Haram ne suka yi garkuwa da su tsawon watanni shida kenan da suka gabata.

Buhari ya bayyana jin dadinsa ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin labarai Malam Garba Shehu ya fitar a Abuja, la’akari da labarin sakin mutanen da aka yi garkuwa da su cikin koshin lafiya, kamar yadda ya ba da umarni a baya.

Ya tabbatar da cewa hukumomin sun nuna kwarewa da bajintar na ceto mutanen.

“Rundunar Sojin kasar nan suna da kwarewa ta musamman kamar kowa. Idan aka ba su goyon baya da ƙarfafawa kamar yadda muke yi, babu wani aiki da ba za su iya cimma sa ba.

“Na yaba musu kwarai saboda wannan gagarumin sakamako da aka cimma,” in ji shugaban.

Yayin da yake nuna jin dadinsa da yadda aka samu nasarar aiwatar da tattaki dan ceto mutanen da sauran wadanda aka yi garkuwa da su, ya kuma taya iyalan wadanda lamarin ya shafa murnar dawowar su da ran su cikin koshin lapia.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here