INEC ta fitar da ka’idojin yakin neman zabe

INEC Mahmood
INEC Mahmood

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC a jihar Kwara ta fitar da ka’idojin fara yakin neman zaben Shekarar 2023.

Kwamishinan zaben Jihar Malam Garba Attahiru, ne ya bayyana hakan ranar Litinin a Ilorin yayin taron masu ruwa da tsaki.

Attahiru, wanda ya samu wakilcin sakataren hukumar ta INEC, Mista Julius Yagba, ya ce an samu nasarar aiwatar da ayyuka 14, yayin da INEC ta fitar da jerin sunayen ‘yan takara na karshe a ranar 20 ga watan nan da muke ciki na Satumba.

Ya ce aiki na gaba da za a yi shi ne fara yakin neman zabe na jam’iyyun siyasa a ranar 28 ga watan Satumbar ban.

Ya kara da cewa an shirya taron ne domin tunatar da masu ruwa da tsaki game da nauyi da kuma abin da ake sa rai a lokacin yakin neman zabe na ofisoshi daban-daban.

A cewar sa, a ranar 28 ga watan Satumbar nan ne za a fara yakin neman zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya, yayin da kuma na gwamna Majalisar Dokokin Jiha sai ranar 12 ga watan Oktoba Mai kamawa 12.

Ya ci gaba da cewa duk wani dan takara da ya baiwa wani mutum ko kungiya makami don tada hankalin al’umma ya aikata laifi kuma za a ci tararsa Naira Dubu 500 ko kuma daurin shekaru uku a gidan yari.

Ya bukaci rundunar ‘yan sandan Najeriya da sauran jami’an tsaro da su sanya ido kan yadda za a gudanar da yakin neman zaben tare da tabbatar da tura jami’ai masu inganci da gogewa domin gudanar da zaben cikin lumana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here