Kasashe yamma kamar Amurka da Burtaniya sun yi kira a gudanar da muhawara a hukumar kare hakkin dan’adam ta Majalisar Dinkin Duniya a kan al’ummar yankin Xinjiang.
Kasashen na son a tattauna a kan zarge zargen cin zarafin da China ke yi wa musulmin Uyghur da kuma sauran kabilu a yankin na Xinjiang.
Wannan yunkuri na zuwa ne bayan wani rahoton da hukumar kare hakkin dan adam ta wallafa cikin watan jiya, wanda ya zayyana irin abubuwan da China ke yi na take hakkin dan’adam da cin zarafi a Xinjiang.
Tuni dai China ta yi watsi da rahoton.
Rahoton dai ya janyo karin kiraye kirayen a dauki mataki a kan mahukuntan China.













































