Kotun koli a ranar Juma’ar nan ta yi watsi da wata karar da ke neman tilasta wa jam’iyyar PDP tsayar da dan takarar ta na shugaban kasa a shiyyar Kudu maso Gabashin kasar nan.
Kotun a hukuncin da ta yanke karkashin jagorancin mai shari’a Adamu Jauro, ta yi fatali da karar a kan cewa ba ta da hurumin sauraro ko shigar da karar.
Cosmos Ndukwe dan takarar shugaban kasa ne a jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Abia ya shigar da karar jam’iyyarsa agaban kotun.
Tsohon dan takarar ya roki me sharia da ya bada wata odar tilastawa jam’iyyar PDP bin tsarin shiyya-shiyya da na karba-karba.
Daga nan sai ya nemi kotu ta ba wa jam’iyyar PDP umarnin tsayar da dan takarar ta na shugaban kasa a shiyyar Kudu maso Gabashin kasa.
Sai dai mai shari’a Jauro ya ce shigar da karar bai dace ba kwata kwata kan cewa tantance ‘yan takara abune da ya shafi jam’iyyun siyasa na cikin gida.













































