Fassarawa:Aminu Bala Madobi-Daga Kano
Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da rattaba hannu kan yarjejeniyar sifirin zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Najeriya da kasar Kuwait.
Ministan Sufurin Jiragen Sama na kasa Hadi Sirika ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan taron majalisar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.
Sirika ya ce yarjejeniyar za ta bude harkokin sufurin jiragen sama tsakanin kasashen biyu bisa tanadin hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa da kasa ICAO.
“Wannan wata dama ce da zata bude damarmaki a shaanin jigilar jiragen sama tsakanin kasashen biyu, bisa ga yarjejeniyar Hukumar Kula da Jiragen Sama ta kasa da kasa ta ranar 7 ga Disamba, 1944, wadda kasashen biyu suka rattaba hannu akai.”
Ministan daganan ya karyata wasu rahotanni da kafafen labarai ke yadawa na cewa an kashe Naira Milyan dubu 14 wajen shirin.
Ya ce jiragen Najeriya gaskiya ne domin za a fara amfani da shi ne domin amfanin yan Najeriya da sauran kasashen Afirka.
Sirika ya ce majalisar ta kuma amince da kwangilar daukar kwararrun masu ba da shawara don gyarawa da tattara bayanan tsaunuka na jiragen sama don manyan gine-gine da matsakaita da ka iya kawo cikas ga ayyukan jirage a Najeriya.
Ya ce kwangilar za ta yi aiki ba tare da kashe kudi masu yawa ba saboda kudaden da aka tara a ciki za a yi amfani da su wajen biyan masu ba da shawara.
Ya ce an yi ta samun hadurran jiragen sama a baya bayannan saboda wurin da aka girke na’urorin sadarwa na da nakasu kamar hakan ta wakana a Jos, Filato. (NAN)











































