Wasu gungun ƴan bindiga, a ranar Asabar, sun yi awon gaba da matafiya da dama a kan titin Benin-owo da ke Ifon, shelkwatar Ƙaramar Hukumar Ose a jihar Ondo.
Ba a iya tantance adadin waɗanda harin ya rutsa da su ba, kamar yadda wasu majiyoyi suka ce wadanda abin ya shafa sun haura 40 yayin da wasu suka bayyana adadin su 32.
Daya daga cikin majiyoyin garin da ta bayyana wa manema labarai faruwar lamarin jiya Lahadi, ta ce wadanda lamarin ya rutsa da su na tafiya ne a cikin wata motar bas ta gaɓar ruwa, daga Benin zuwa jihar Ondo, inda suka je bikin binne mamaci.
“Amma da isa yankin Ifon, ƴan ta’addan su ka yi kwanton ɓauna tare da kaɗa duk mutanen da ke cikin motar cikin daji.
“Dukkan mutanen da ke cikin motar an yi garkuwa da su ne tun jiya (Asabar) kuma babu wanda ya ji komai game da su tun daga lokacin,” in ji wani ɗan uwan wanda abin ya shafa.
Da ta ke tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, jami’ar hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Ondo, SP Funmilayo Odunlami, ta ce ba za ta iya tantance adadin wadanda abin ya shafa ba.
A cewar PPRO ɗin, jami’an rundunar da sauran jami’an tsaro a jihar sun fara neman wadanda abin ya shafa a dajin.
“Tuni jami’an mu da sauran jami’an tsaro su ka shiga dajin domin ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su ba tare da sun ji rauni ba, yayin da aka fara gudanar da bincike kan lamarin,” in ji Odunlami.













































