Ba wani mataki na nan take da zamu iya dauka don magance matsalolin hukumar dake kula da zirga zirgar jiragen sama ta kasa- Hadi Sirika

hadi sirika 1
hadi sirika 1

Ministan hukumar dake kula da zirga zirgar jiragen sama ta kasa, Hadi Sirika, ya ce ba wata hanya ta gaggawa da hukumar zata iya bi domin magance matsalolin da su ka addabi hukumar.

Hadi ya bayyana hakan ne yayen wani taron gaggawa da kungiyar kamfanonin jiragen sama ta Najeriya AON, a Abuja ranar Talata.

Ministan ya tabbatar da cewa tarin matsalolin da hukumar ke fama da su sun fi karfin hukumar ta magance su a yanzu.

Ya kara da cewa ba wata gajeriyar hanya da hukumar zata iya bi don maganci matsalolin, saboda abin ya shafi duniya baki daya.

“ Rashin man jirgi abu ne wanda ya shafi duniya baki daya, ba wai iya Najeriya ba, ya shafe kasar America, New Zealand da sauran kashashen duniya, kuma ma Najeriya bata iya samar da man jirgi” Inji shi.

Yayin jawabin sa, shugaban kungiyar masu kamfanonin jiragen sama ta Najeriya AON, Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina, ya koka kan yacce man jirgi yai tashin doran zabuwa, daga N180 duk lita zuwa N1000 a halin yanzu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here