Yan bindiga sun kai hari Kauyen Gunduma a Jihar Taraba

Bandits Bandits
Bandits Bandits

A ranar Alhamis ne ‘yan bindiga suka kai wani sabon hari garin Gunduma dake jihar Taraba.

Wani mazaunin garin Nuradden Garba ya tabbatarwa da jaridar Solacebase cewa, ‘yan bindigar sun yiwa garin kawanya a kan Babura tare da harbe harben bindiga.

Yace ya zuwa wannan lokaci al’ummar garin suna cikin fargaba, domin kuwa a cewarsa har yanzu sun tunanin yan bindigar basu fita daga kauyen ba.

Wakilin Solacebase ya yi kokarin jin ta bakin kakakin rundinar ‘yansandan jihar Usman Abdullahi, inda ya tabbatar masa da cewa suna kan gudanar da bincike akan lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here