Yan Bindigar da suka yi garkuwa da Dan majalisar Jihar Anambra sun sare Kansa

Okechukwu Okoye 600x381 1
Okechukwu Okoye 600x381 1

Wasu ‘yan bindiga sun sare kan dan majalisar da ke wakiltar mazabar Gwamna Chukwuma Soludo a majalisar dokokin jihar Anambra, Hon Okechukwu Okoye.

An gano kan Okoye ne ranar Asabar a Nnobi da ke karamar hukumar Idemili ta Kudu a jihar Anambra inda masu garkuwa da mutane suka rataye shi.

Ba a ga gawarsa a inda aka rataye kan ba, lamarin da ya kara nuna alamun wadanda suka kashe Dan majalisar sun tafi da gawar.

An yi garkuwa da shi ne tun a makon jiya lokacin suna tare da daraktan yakin neman zabensa, Cyril Chiegboka, a cikin motarsa kirar Toyota Sienna.
Rahotanni sun bayyana cewa daga baya jami’an ‘yan sandan sun samo motar tare da ci gaba kokarin ceto dan majalisar.

Tuni dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, Ikenga Tochukwu ya tabbatar da mutuwar Okoye, yana mai cewa: “An tsinci kansa a kan titin Nnobi a yau (Asabar). Har yanzu dai babu wanda ake tuhuma.”

A ranar Litinin ne Gwamna Soludo ya yi kira da a gaggauta sakin Okoye da Chiegboka ba tare da wani sharadi ba.

Soludo, a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Mista Christian Aburime ya fitar, ya yi Allah wadai da irin sace-sacen da ake yi da kuma karuwar rashin tsaro a jihar Anambra.

“Gwamnan ya yi Allah-wadai da yawaitar tabarbarewar tsaro a fadin jihar a baya-bayan nan inda ake kai wa al’umma hari tare kuma da hallakasu.

“Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da gwamnati ta tattauna da masu ruwa da tsaki don maido da zaman lafiya da tsaro a jihar,” in ji sanarwar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here