Ba zamu saurarawa duk wanda aka samu da tada tarzoma a jihar Bauchi ba- Sanata Bala Muhammad

Kauran Bachi
Kauran Bachi

Gwamnatin jahar Bauchi ta yi alkawarin gudanar da bincike tare da daukar matakin ba sani ba sabo kan wadanda ke da hannu wajen tayar da rikicin addini a karamar hukumar Warji dake Jahar Bauchi.

Gwamnan jihar Sanata Bala Muhammad Abdulkadir ne ya sanar da hakan ranar asabar din da ta gabata a fadar hakimin Warji yayin daya kai ziyarar gani da ido, inda yace tuni hukuma ta kama wacce ake zargi da tada husumar mai suna Rhoda Jatau wacce ba ƴar asalin karamar hukumar bace.

“Insha Allahu Jami’an tsaro kamar yadda suka bani tabbaci suna nan zasu bude idanu da kunnuwa cewa duk wanda yake da hannu a tada tarzoma ko husuma ba za a saurara masa ba”. Inji Gwamnan.

Ya kuma bukaci hakimin gundumar ta Warji Alhaji Alhassan Sama’ila da shugaban karamar hukumar Hon. Adamu Muhammad Dan-Jummai, da su kara sanya ido, tare da tabbatar da an hukunta wanda ya yi laifi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here