Kasar Saudiyya zata gudanar da Idi ranar Litinin sakamakon rashin ganin wata a ranar Asabar

Saudi moon 600x381 1
Saudi moon 600x381 1

Hukumomi a Kasar Saudiyya sun ayyana ranar Litinin 2 ga watan Mayu a matsayin ranar da za a gudanar da Sallar Idi sakamakon ba a ga watan Shawwal a ranar Asabar ba.

Ba a iya ganin jinjirin watan na Shawwal daga dakin duban wata na Tamir a jami’ar Majmaah da ke Hautat Sudair a ranar Asabar din ba.

A cewar jaridar Saudi Gazette hakan na nufin ranar Lahadi 1 ga watan Mayu ita ce ranar karshe ta watan Ramadan kuma ranar Litinin 2 ga watan Mayu ita ce ranar farko ta watan Shawwal.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here