Sanata Barau ya kaddamar da Kwamitin Yakin Neman Zabe na Yankin Kano ta Arewa, ya yi kira da a yi gangami gida-gida ga duk ‘yan takarar APC

IMG 20260905 WA0178 1 750x430

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya kaddamar da Kwamitin Yakin Neman Zabe na Yankin Kano ta Arewa gabanin zaben Shugaban Kasa da na ‘Yan Majalisar Kasa da za a yi a ranar 16 ga Janairu 2027, kamar yadda Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta tsara.

Sanata Barau, wanda ke wakiltar Kano ta Arewa a Majalisar Dattawa, ne ya sanar da sunayen mambobin kwamitin a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan yada labarai, Ismail Mudashir, ya fitar a ranar Asabar.

Injiniya Rabiu Sulaiman Bichi, Daraktan Hukumar Raya Kogunan Hadeja Jama’are kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, ne Shugaban kwamitin.

Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Makoda, zai zama Mataimakin Shugaba, yayin da Surveyor Nadu Yahaya, Shugaban Majalisar Gudanarwa ta Kwalejin Kimiya da Fasaha ta Tarayya Bauchi, ne Sakataren kwamitin.

Dr. Kabiru Ado Zakirai, Hon. Ahmed Haruna Bichi da Hon. Idris Unguwar Rimi za su zama Mataimakan Sakatare I, II da na III.

Tsohon ‘dan Majalisar Wakilai, Hon. Farouk Lawan, zai zama Mataimakin Shugaba na I, Hon. Saidu Garba Getso Mataimakin Shugaba na II, sai kuma Hon. Badamasi Ayuba Mataimakin Shugaba na III.

Alhaji Yusuf Tumfafi zai zama Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben.

Hon. Yusuf Tabuka, Hon. Auwalu Ibrahim Danzabuwa, Hon. Ali Ado Bagwai da Hon. Ali Gumawa za su zama Mataimakan Darakta Janar I, II, III da na IV.
Shugabannin Kananan Hukumomi 13 da Mataimakansu za su zama shugabanni da mataimaka a kananan hukumominsu.

Mambobin Kwamitin Yankin sun hada da dukkan tsoffin Gwamnoni da Mataimakan Gwamnoni Sanatoci da ‘Yan Majalisar Wakilai da masu ci daga yankin.

Duk ‘yan takarar APC na Majalisar Wakilai da Majalisar Dokokin Jihar Kano daga yankin.

Duk tsoffin da masu rike da mukamai a matakin Jaha da Tarayya daga yankin.

Dukkan Exco na Jaha, na Yankin, Shugabannin Kananan Hukumomi, Shugabannin APC na Kananan Hukumomi, Shugabannin dattawa na APC na Kananan Hukumomi da duk tsoffin ‘yan majalisu da masu ci da masu mukamai daga gwamnatin tarayya da jaha daga yankin.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya umarci dukan mambobin kwamitin yakin da su kai gangamin APC zuwa kowane lungu da sako na Kano ta Arewa, tare da samar da goyon baya mai yawa ga duk ‘yan takarar APC.

Ya jaddada cewa ayyukan gwamnati suna magana da kansu, samar da tasiri a sassa masu muhimmanci da suka shafi rayuwar ‘yan yankin.

Saboda haka Sanata Barau ya bukaci kwamitin yakin da su kai sakon nasarorin da aka samu ga mutane, tare da tabbatar da samun goyon baya mai yawa ga APC a zabe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here