Ku daina magana a kan takardar shaidar Tinubu, ku tallata ra’ayoyinku ga ‘yan Najeriya – Ndume ga ‘yan adawa

Ali Ndume 720x430

Sanata Ali Ndume ya yi kira ga jam’iyyun adawa da su mayar da hankali kan ayyukan Shugaba Bola Tinubu maimakon takardun shaidar karatunsa, yayin da harkokin siyasa da zaben Janairu 2027 ke kara zafi.

Ndume, jigo a jam’iyyar APC kuma Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattijai, ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Abuja.

Ya bayyana cewa dambarwar da ake yi kan takardun shaidar Tinubu ba ta da amfani kuma tana dauke hankali ne kawai daga ainihin batutuwan da suka kamata ayi.

Ndume ya ce, “Labarin da ake yadawa game da takardar shaidarsa yana dauke hankali. Abin da ya kamata ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun adawa su yi shi ne su fada wa ‘yan Najeriya abin da za su iya. Mene ne manufofinsu na tattalin arziki? Me za su iya yi da ya fi na Shugaba Tinubu?

“Yakamata su kalubalanci manufofinsa na tattalin arziki da kuma yadda gwamnatinsa ta magance matsalar tsaro. Shugaban kasar ya shafe shekaru uku yana kan mulki, don haka me zai sa takardun shaidarsa su zama babban abin tattaunawa?”

An sake samun damuwa tsakanin jiga-jigan ‘yan adawa bayan bincike ya nuna cewa a cikin fam din EC9 da Tinubu ya mika, an bar gurbi na makarantun firamare da sakandare ba a cike ba.

Shugaban kasar ya lissafa Digiri na farko (B.Sc) a fannin Gudanar da Kasuwanci  daga Jami’ar Jihar Chicago, wanda ya samu a shekarar 1979. Ya hada da takardar shaidar digirinsa da takardar shaidar kammala hidimar kasa (NYSC).

Sai dai Ndume ya ce shugaban kasar ya cika ka’idojin doka.

Yayin da yake ambaton Sashe na 131(d) na Kundin Tsarin Mulki na shekarar 1999, ya ce, “Kundin tsarin mulki ya kayyade mafi karancin cancantar ilimi ne kawai. Bai ce lallai sai takardar shaidar makarantar sakandare ba.”

Sashen ya tanadi cewa dole ne dan takara ya kasance “ya yi karatu akalla zuwa matakin Takardar Shaidar Makaranta ‘School Certificate level’ ko makatancinsa.”

Ya kuma lura cewa tuni kotuna suka warware batutuwan da suka shafi cancantar Tinubu bayan zaben 2023.

Dan majalisar ya bukaci jam’iyyun adawa da su daukaka darajar yakin neman zaben.

Tsohon Jagoran Majalisar Dattijan ya kara da cewa, “Yayin da muke zurfafa cikin yakin neman zabe, ya kamata ‘yan adawa su daukaka batutuwan da suka wuce na kashin kai.

“Kamar yadda Eleanor Roosevelt ta taba fada, manyan zukata suna tattauna ra’ayoyi, matsakaitan zukata suna tattauna abubuwan da suka faru, kananan zukata kuma suna tattauna mutane.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here