Gwamna Uba Sani ya zabi Jerry Adams a matsayin abokin takararsa a 2027

jerry adams

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya zabi Jerry Adams, Shugaban Hukumar Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS), a matsayin abokin takararsa a zaben gwamna na 2027.

“Bayan shawarwari, nazari mai zurfi da addu’o’i mai yawa, ina farin cikin sanar da zabin Mista Jerry Adams, FCTI, FNIM, CNA, a matsayin abokin takarata a Zaben Gwamnan 2027,” in ji gwamnan a shafinsa na X a ranar Talata.

Wannan zabi shi ne karo na farko cikin shekaru 7 da jam’iyyar APC mai mulki ta fitar da Kirista a matsayin dan takarar mataimakin gwamna a Jihar Kaduna. Wannan ya nuna sabon sauyi daga tikitin Musulmi-Musulmi da jam’iyyar ta yi a zaben 2019 da 2023.

A cewar gwamnan, wannan zabi yana nuna kudurin gwamnatin sa na hada kowa, adalci, daidaito da wakiltar kowa daidai a fadin jihar.

“Wannan shawarar ta wuce zabin dan takarar mataimakin gwamna kawai., wani sabn tabbaci ce na dabi’un da suka jagoranci gwamnatin mu tun bayan da na dauki rantsuwar kama aiki a ranar 29 ga Mayu 2023; dabi’un hada kowa, adalci, daidaito da karfi kan cewa kowane dan Jihar Kaduna ya cancanci jin yana cikin gida,” in ji gwamnan.

“A yau, mun dauki wani muhimmin mataki a tafiyar mu ta gina Jihar Kaduna mai hadin kai, zaman lafiya da tafiya da kowa.

Bayan shawarwari, nazari mai zurfi da addu’o’i, ina farin ciki na sanar da zabin Mista Jerry Adams, FCTI, FNIM, CNA, a matsayin… pic.twitter.com/CQsU3xQCLQ
— Sanata Uba Sani (@ubasanius) Yuli 28, 2026”

Ya ce wannan shawara ta nuna imaninsa na ba da sakamako ga kwazo, mutunci da hidima ta gaskiya.

Gwamna Sani ya bayyana Adams a matsayin ma’aikacin gwamnati mai nasara, wanda ke gina cibiyoyi kuma masanin tattara haraji da aka girmama. Jagorancinsa a KADIRS ya karfafa karfin kudin jihar ta hanyar sauye-sauye da suka inganta harajin cikin gida da gudanar da kudin gwamnati.

“Ta hanyar sabbin dabaru, gaskiya da sana’a, ya taimaka wajen karfafa karfin kudin mu, wanda ya bai wa gwamnati damar kara zuba jari a ilimin ‘ya’yan mu, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, noma da sauran muhimman fannoni da ke inganta rayuwar al’ummar mu,” in ji Sani.

Gwamnan ya ce zabin Adams ya karfafa hangen nesansa na gina Jihar Kaduna mai hadin kai, zaman lafiya da wadata inda kwazo, sana’a da hali ke zama ginshikin jagoranci. Ya kara da cewa gwamnatin sa ta kuduri aniyar tabbatar kowane dan kasa ya ji yana cikin gida ba tare da la’akari da asalin sa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here