Wata kungiya mai suna Gawuna/Garo Professional Political Network (GAPON) ta sha alwashin tattara kuri’u miliyan 1 domin samun nasarar Yan takarar Gwamna da Mataimakinsa na jam’iyyar APC, a zaben 2023 mai zuwa.
Shugaban kungiyar ta GAPON, Sadi Garba Sa’id, ya bayyana haka a ranar Juma’a, yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano kan ayyukansu inda ya bayyana cewa kungiyar ta samu mambobi daga bangarori daban-daban da Kuma kungiyoyi a kananan hukumomi 44 na jihar.
A cewarsa, kofar kungiyar a bude take ga masu irin wannan tunani Kama daga daidaikun mutane da kungiyoyi da masu ruwa da tsaki na al’umma kan su ba mu goyon baya wajen ganin GAWUNA da GARO sun zama ‘yan takara mafi karbuwa a Jihar Kano.
Ya kuma yi nuni da cewa za su yi amfani da kafafen sada zumunta na zamani don yada manufofin Gawuna da Garo.
Ya ce: “Bari mu zama kan gaba wajen yada manufofin Gawuna da Garo a kafafen sadarwa na zamani da kuma zaburar da wasu kwararru domin su shiga a dama da su. Mu kara samar da kwararru don ganin nagartattun Yan takarar mu na APC sun Kai ga ci.”
Ya kuma yi nuni da cewa, GAPON ta himmatu wajen jawo hankalin wadanda zasu kada kuri’a miliyan 1 a fadin Kano kan batutuwan da suka shafi ci gaba mai dorewa da sake fasalin kasa tare da hada hannu da masu ruwa da tsaki da kuma tsara lokaci don ci gaban matasa ta hanyar tsare-tsare da gudanar da ayyuka.
“Bari mu jaddada soyayyarmu da nuna biyayyarmu ga siyasar Gawuna da Garo mu Kuma sanya hakan a zukatan kwararru Mata da matasa da tsofaffi ta hanyar yin gangami a kananan hukumomin 44 na jihar Kano.
“Bari mu shiga harkokin zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da kuma kyawawan dabi’u da nufin jawo hankalin mutane da yawa zuwa tafiyar mu a jihar Kano.”










































