Yanzu-Yanzu: LPPC ta dakatar da Mike Ozekhome daga matsayin Babban Lauyan Najeriya SAN

Mike Ozekhome 1

Kwamitin da ke bayar da mukamin SAN da kula da da’a (LPPC) ta dakatar da Mike Ozekhome daga matsayin Babban Lauyan Najeriya (SAN), har sai an kammala bincike kan da’a da ake yi masa.

A cikin wata sanarwa da Babban Rijistaran Kotun Koli, Kabir Akanbi ya fitar a ranar Laraba, ya ce an dauki wannan hukuncin ne a taron kwamitin karo na 173 da aka gudanar a ranar 23 ga Yuni.

LPPC ta ce an amince da dakatarwar dogaro da sashe na 26(6) na ka’idojin ba da matsayin Babban Lauyan Najeriya da dukkan al’amuran da suka shafi matsayin.

A cewar kwamitin, dakatarwar za ta ci gaba da aiki har sai an yanke hukuncin karshe kan shari’ar ladabtarwa da ke gaban karamar kwamitin Ladabtarwa da Da’a, da sauran shari’u masu alaka da ita.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here