Zargin Almundahana: Kotu ta dage shari’ar Ganduje, matarsa da sauran mutum 6

R L Abdullahi Ganduje and Wife Hafsat 750x430

Shari’ar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, da sauran mutum 7 kan zargin almundahana ta fuskanci cikas a ranar Laraba, yayin da Babbar Kotun Jihar ta dage shari’ar zuwa 14 ga Oktoba.

Ganduje yana fuskantar shari’a tare da matarsa, Hafsat Umar kan tuhume-tuhume 11 da suka shafi cin hanci, makirci, almundahana da karkatar da kudaden jama’a da suka kai biliyoyin naira.

Sauran wadanda ake kara a shari’ar su ne Abubakar Bawuro, Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd da Lasage General Enterprises Ltd.

Yayin zaman sauraro, dukkan bukatun da aka gabatar, lauyan masu gabatar da kara, Mista Victor Oni, ya shaida wa kotu cewa a shirye jihar take domin cigaba da shari’ar.

Oni ya shaida wa kotu cewa masu gabatar da kara sun shigar da bukatar a ranar 15 ga watan Mayun 2026, kuma sun nemi izinin janye wata bukata da suka gabatar a baya a ranar 31 ga Maris 2026.

Ya roki kotun ta sauya bukata ta baya wadda ke dauke da kwanan wata ranar 15 ga Mayu, da shaidar kotu da sabon rubutaccen jawabi a kan hurumun kotun da bukatar dakatar da shari’ar na wanda ake kara na 6.

Lauyar Ganduje, matarsa da dansa, Mrs Lydia Oluwakemi-Oyewo, ta shaida wa kotu cewa b angaren da take karewa ya shirya cigaba da shari’ar kuma ba su da wata korafi kan bukatar masu gabatar da kara.

Oluwakemi-Oyewo, wadda ta wakilta Chief M.N. Duru (SAN), lauyan wanda ake kara na 3 da na 7, ta ce ita ma ba ta da wani korafi kan bukatar masu gabatar da kara.

Hakazalika, lauyan wanda ake kara na 5, Mista Muhammad Shehu, ya ce ya shirya cigaba.

Lauyan wanda ake kara na 6, Mista Abubakar Ahmad, ya sanar da kotu cewa ya shigar da sanarwar Rashin Hurumi, shaidar kotu da rubutaccen jawabi, sannan ya nemi a ba shi ranar sauraron bukatar.

Lauyan wanda ake kara na 8, Mista Abdulrazaq A. Ahmed, ma ya shaida wa kotu cewa ya shirya cigaba.

Mai shari’ar da ke jagorantar zaman, Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu, daga baya ta kore bukatar masu gabatar da kara bisa sanarwa da ta dauki ranar 31 ga Maris 2026.

Sai ta dage shari’ar zuwa ranar 14 ga Oktoba domin sauraron ‘preliminary objection’ na wanda ake kara na 6. NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here