Gwamnatin Taraba ta rage albashin ‘yana shara daga Naira 15,000 zuwa Naira 10,000

Gov. Agbu Kefas

Gwamnatin Jihar Taraba ta rage albashin mambobin shirin tsaftace Taraba na “Operation Keep Taraba Clean”, da aka fi sani da ‘Yan Shara, daga Naira 15,000 zuwa Naira 10,000.

Dalilin da ta bayar shi ne bukatar daukar ma’aikatan gwamnati sababbi da aka dauka a ma’aikatur gwamnatin jihar.

Shugaban Hukumar Muhalli da Tsabta ta Jihar Taraba, Hon Illiya Kefas ne ya tabbatar da lamarin yayin da yake zantawa da manema labarai a Jalingo.

A cewarsa, an dauki wannan mataki ne bisa umarnin Gwamna Agba Kefas da nufin sarrafa albarkatun da ke hannu, sakamakon daukar ma’aikatan da aka yi kwanan nan a ma’aikatun gwamnatin jihar da ta kananan hukumomi.

“Haka ne, ba mu biya ‘yan shara Naira 15,000 ba wannan watan, mun biya kowannensu Naira 10,000,” Hon. Kefas ya bayyana.

Gwamnatin jihar ta fara daukar ‘yan sharan ne a shekarar 2023 da alawus na wata-wata na Naira 20,000.

Sai dai a watan Maris 2024, an ce an tilasta musu su yarda da rage Naira 5,000 ko su bar aikin, hakan ya sa albashinsu ya sauka zuwa Naira 15,000.

Rahotanni sun nuna cewa ma’aikatan sun karbi Naira 10,000 a watan Mayu 2026, wanda hakan wani ragi ne daga adadin da aka tattauna a baya.

Da yake bayanin dalilin hakan, Kefas ya ce jihar ta daidaita alkawuranta na kudi biyo bayan daukar sabbin ma’aikata da yawa.

A cewarsa, karancin kudin da ke zuwa daga Asusun Tarayya ma ya taimaka wajen daukar wannan mataki.

Dangane da wannan sabon umarni, rahotanni na nuna cewa albashin masu sharar na wata-wata na iya kara sauka zuwa kusan Naira 7,500 idan ragin kashi 50 cikin 100 ya shafi tallafin Naira 15,000 da aka tattauna a baya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here