‘Yan sanda sun fara bincike kan mutuwar matashin dan kasuwa a gidan budurwarsa a Kano

IMG 20260620 WA0131 1 750x430

Matashin dan kasuwar, Isma’il Makaye, ya rasu a karkashin yanayi mai cike da shakku a gidan budurwarsa, shahararriyar tauraruwa a TikTok kuma mai rawar Solo, Fati Cele, a Jihar Kano.

A cewar majiyoyi, lamarin ya faru ne da safe ranar Juma’a lokacin da Fati Cele ta ce ta shigar da korafi bayan da gobara ta tashi a gidanta.

Makwabtan da suka amsa kiran taimako, sun ce sun tarar da Makaye kone a jikinsa sannan kuma da alamun jini.

Majiyoyi kusa da marigayin sun ce an garzaya da shi Asibitin Nassarawa, inda daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.

An binne shi daga baya a yankin Unguwa Uku Yan Awaki ta Kano.

Da yake zantawa da SolaceBase kan lamarin, jami’in wulda da jama’a na rundunar ‘Yan Sandan Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce Fati Cele tana tsare yayin da rundunar ta fara bincike.

Kiyawa ya ce Fati, wadda itama ta raunin kuna a hannunta, an kai ta asibiti don magani.

SolaceBase ta rawaito cewa gawar marigayin tana dauke da kuna da raunuka, yayin da takalmin Fati guda daya yake da alamun jini.

Abokan marigayin da tauraruwar TikTok sun ce matanen sun taba samun matsalar soyayya kuma sun rabu kafin su sake yin sulhu kwanakin baya.

Lamarin ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda mutane da yawa ke kira ga hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike na gaskiya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here