Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin ya rubuta wa Ministan Ayyuka, Dave Umahi, yana rokon a soke kwangilar aikin hanyar Kano–Gwarzo–Dayi saboda rashin kokarin da ya dace na kamfanin da ke aikin.
SolaceBase ta ruwaito cewa aikin ya hada da fadada hanyar Kano–Gwarzo–Dayi mai nisan kusan kilomita 100 wanda yake hannu daya zuwa hanya mai hannu biyu domin inganta sufuri da saukake jigilar kayayyakin noma daga kauyuka zuwa kasuwanni a jihohin makwabta.
A cikin wata wasika da aka fitar, SolaceBase ta tabbatar a ranar Alhamis wadda Sanata Barau ya sanya hannu da kansa, sanatan ya bayyana damuwa sosai kan aikin CGC Nigeria Limited, kamfanin da ke gudanar da aikin, wadda ta isa ofishin Ministan Ayyuka ranar 8 ga Yuni 2026, inda ya lura cewa duk da biliyoyin da aka ba kamfanin.
Wasikar mai kwanan wata 4 ga Yuni 2026, wani bangarenta ya ce ”Baiwa hanyar Kano-Dayi muhimmanci don ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin jihohin Kano, Katsina da Kebbi, abin damuwa ne cewa kamfanin ya gaza samun ci gaba mai gamsarwa duk da ware Naira biliyan 19 da Naira biliyan 37 ga aikin a karkashin Dokar Kasafin Kudi ta 2025 da 2026. Wannan rashin ci gaba akai-akai ya haifar da wahala mara amfani ga mazauna, matafiya da sauran masu amfani da hanya.
Sanata Barau ya jaddada cewa ci gaba da jinkirin kammala aikin ya yi mummunar illa ga mazauna, matafiya da harkokin tattalin arziki a kan wannan hanyar, sannan ya nemi Ministan Ayyuka ya dauki mataki na gaggawa.
“Wannan rashin ci gaba da aikin ya haifar da wahala mara amfani ga mazauna, matafiya da sauran masu amfani da hanya.












































