HOTUNA: Gobara ta cinye kasuwar kayan gida, daki da ofis a Kano

IMG 20260612 WA0082

Wata Mummunar gobara ta lalata sananniyar kasuwar kayan gida da kayan daki da kuma na ofis da ke kan Titin Murtala Mohammed a Kano, inda ‘yan kasuwa suka yi mummunar asarar miliyoyin naira.

Bisa ga bayanan da aka samu, gobara ta tashi da kamar misalin karfe 10:00 na dare a ranar Alhamis.

Shaidu sun shaida wa SolaceBase cewa wutar ta yadu cikin sauri ta cinye dukan kasuwar, ta mayar da shaguna da kayan da ke cikinsu toka.
Daya daga cikin ‘yan kasuwar da lamarin ya shafa, Kamal Salisu, ya shaida wa SolaceBase cewa wutar ta cinye dukan kasuwar gaba daya, lamarin da ya haifar da asarar kayayyaki masu darajar miliyoyin naira.

IMG 20260612 WA0082 IMG 20260612 WA0081 768x1024
“Har yanzu ba a gano musabbabin gobara ba, yayin da ‘yan kasuwa ke kallon abin ba tare da sanin mafita ba, jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano na ci gaba kokarin kashe wutar.”
Dan kasuwar ya kara bayyana cewa wutar ta yadu zuwa wani gini da ke kusa da shi wanda ofishin kamfanin jigilar kayayyaki na kasa da kasa DHL ke ciki, inda ta lalata kuma ta kone wani bangare na rufin ginin.

SolaceBase ta ruwaito cewa kasuwar da lamarin ya shafa, wadda ke tsakanin ginin DHL da FCMB a kan Titin Murtala Mohammed, sananniya ce da ake sayar da kayan gida da na ofis, ciki har da kujeru, kafet, na’urorin sanyaya daki, katifu, firiji, talabijin, da sauran kayan ado na ciki gida da ofis.

SolaceBase ta yi kokarin tuntubar Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano domin jin ta bakin sa, amma duk kokarin ya ci tura saboda layin wayar sa ba a samu ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here