PDP ta kafa kwamitocin sauraron korafe-korafe kan takaddamar zaben fidda gwani

PDP

Jam’iyyar PDP ta kafa kwamitocin da za su saurari kararraki domin magance koke-koke da korafe-korafen da suka taso daga zaben fidda gwani na kujerar shugaban kasa, gwamnoni, ‘yanmajalisar jiha da na tarayya.

An kafa kwamitocin ne don tabbatar da gaskiya, adalci da dimokuradiyyar ciki a tsarin zaben jam’iyyar.

A cikin sanarwar da Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar na Kasa, Jungudo Mohammed, ya fitar a ranar Alhamis, ya ce kwamitocin za su nazarci korafe-korafen da ’yan takara da sauran masu ruwa da tsaki wadanda ba su gamsu ba suka gabatar.

“Kwamitocin shigar da karar za su saurari da yin nazari kan korafe-korafen da ’yan takara da masu ruwa da tsaki wadanda ba su gamsu da sakamakon zaben fidda gwani ba suka shigar.

“Za su kuma bayar da shawarwari bisa ga Kundin Tsarin Mulkin jam’iyyar, jami’an zabe da sauran tanadin doka da suka dace,” in ji shi.

Mohammed ya ce wannan mataki ya nuna jajircewar PDP wajen gudanar da tsarin zaben ’yan takara masu inganci kafin zaben da ke tafe.

A cewarsa, Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Abdulrahman Mohammed, zai jagoranci kwamitin korafin kara na gwamnoni da shugaban kasa. Samuel Anyanwu na daga cikin mambobin kwamitin.

Mohammed ya kara da cewa Suleiman Atolagbe zai jagoranci kwamitin karar jihohi da majalisar kasa.

Kwamitin kara na jihohi da majalisar kasa da ke da mambobi 9 zai zauna a ranakun 8 da 9 ga Yuni.

Kwamitin zai yi zama a Babban Zaure na Kwamitin Gudanarwa na Kasa NWC da ke Abuja.

Mohammed ya kara bayyana cewa kwamitin sauraran karar gwamnoni da shugaban kasa da ke da mambobi 24 zai zauna a ranar 10 ga Yuni.

Ya ce kwamitin ma zai zauna a hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here