Shugaba Bola Tinubu zai yi jawabi ga Hadakar Zaurukan Majalisun Kasa a ranar 12 ga Yuni a matsayin wani bangare cikin bukukuwan cika shekaru 27 da Najeriya ta ke murnar ranar Dimokuradiyya.
An bayyana hakan a ranar Talata yayin kaddamar da kwamitin ministoci na musamman IMC da ke da alhakin shirya bikin na kasa.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ne ya kaddamar da kwamitin a Cibiyar Shehu Shagari dake Abuja.
Akume ya ce jawabin shugaban kasar zai kasance daya daga cikin manyan abubuwan da aka tsara a lokacin bikin tunawa da ranar.
Ya bayyana Ranar Dimokuradiyyar a matsayin wata dama ta tunawa da sadaukarwar da ’yan Najeriya da suka yi a gwagwarmayar tabbatar da dawo da mulkin dimokuradiyya.
Akume ya yaba wa ‘Yan kishin kasa bisa gwagwarmayar 12 ga Yuni 1993 da kuma marigayi Moshood Kashimawo MKO Abiola.
Ya bukaci mambobin kwamitin da su fara aiki nan take, inda ya bayyana cewa suna da kwanaki 10 ne kacal kafin bikin.
Ya ce a wannan shekara za su nuna yanayin da kasa ke ciki da kuma himmar gwamnati kan dorewar kashe kudi.
Sauran abubuwan da aka amince da su a bikin cika shekaru 27 na Ranar Dimokuuradiyya, sun hada da taron manema labarai na duniya a ranar 4 ga Yuni.
Shirin zai kuma kunshi sallar Juma’a ta musamman a ranar 5 ga Yuni, da babban ibadar coci a ranar 7 ga Yuni.
Za a gudanar da lacca ta musamman kan Ranar Dimokuradiyya a ranar 9 ga Yuni, yayin da aka tsara shirye-shirye na matasa da mata a ranar 10 ga Yuni.
Shugaban kasa zai gabatar da jawabi a ranar 12 ga Yuni. Inda za a rufe da babban biki na gala na Ranar Dimokuradiyyar a ranar 12 ga Yuni.












































