Jerin sunayen ‘yan takarar maslaha a NDC ta Kano a zaben 2027

NDC NDC

Jam’iyyar NDC ta fitar da jerin ’yan takarartar maslaha gabanin babban zaben 2027 a Jihar Kano, inda ta bayyana tsohon mataimakin gwamna Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin dan takarar gwamna.

Haka zalika, sauran sunayen da jam’iyyar ta fitar a Kano, akwai tsohon mataimakin gwamna Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin dan takarar yankin Kano ta Tsakiya ta Majalisar Dattawa, yayin da Injiniya Sunusi Usman Dambatta da Kasim Ibrahim Bataiya aka zabe su a matsayin ’yan takara a Kano ta Arewa da Kano ta Kudu.

SolaceBase ta ruwaito cewa jam’iyyar ta kuma fitar da ’yan takararta na kujeru Majalis 24 na jihar. Daga cikin manyan ‘yan takarar akwai tsohon dan Majalisar Wakilai Mustapha Bala Dawaki na kananan hukumomin Dawakin Kudu/Warawa, Aminu Sulaiman Goro na Fagge da AVM Ibrahim Umar na karanar hukumar Dala, da sauran su.

Bugu da kari, jam’iyyar ta fitar da sunayen ’yan takarartar 40 maslaha a Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Daga cikin wadanda aka zaba akwai Sani Shehu Ibrahim na Ajingi, Yakubu Yusuf Baita na Albasu, Dr. Nura Jafar na Bagwai/Shanono, Ali Muhammad Adakawa na Dala, Abdulkadir Ahmad Getso na Gwarzo, da Alkasim Hussaini na Wudil ta Jiha.

Ga jerin sunayen cikakke a ƙasa:

IMG 20260530 WA0304 768x1007

IMG 20260530 WA0305 768x1072

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here