Archbishop ya shawarci Jonathan da ya guji tsayawa takara a zaben shugaban kasa

IMG 20260516 WA0010 2 768x513 1 750x430

Archbishop Metropolitan kuma Firimatar Cocin Najeriya (Anglican Communion), Mafi Girma Rev. Henry Ndukuba, ya shawarci tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan da ya yi watsi da kiraye-kirayen tsayawa takara a zaben shugaban kasa na 2027.

​Ndukuba ya ba da shawarar ne yayin gabatar da jawabin sa a Taron Farko na 13th Synod na Diocese na Abuja a ranar Asabar a Abuja.

Ya yi gargadin cewa dawowa cikin siyasar jam’iyya na iya rage daraja da mutuncin da yake da shi na dan siyasa babba da kuma mutunta shi da duniya ke yi a yanzu.

A cewar malamin, Jonathan ya riga ya tabbatar da kima da gogewa a tarihi a matsayin alamar cikar ta dimokradiyya da shugabanci na lumana, musamman bayan yadda ya amince da kayen a tarihi bayan zaben shugaban kasa na 2015.

“Ba ma son ka lalata wannan kyakkyawan suna, don Allah ka tsaya a gefe a yanzu, ka bari su yi wasan su, ka zama dattijon kasa kamar yadda ya kamata.

“Muna gode wa Allah saboda rayuwarka, ba kawai ga Najeriya ba har ma da yankin Yammacin Afirka, ECOWAS, da Afirka.

“Kai alama ce da ya kamata ta tsaya tsaye, kai ne bege ga karninmu, cewa yana yiwuwa mu zama masu dabi’a, mu yi jagoranci da gaskiya, kuma yana yiwuwa mu bar gadon da ya dace ga wadanda za su zo bayanmu,” in ji Ndukuba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya bayyana cewa ​Jonathan, wanda ya yi rike matsayin shugaban Najeriya daga 2010 zuwa 2015 a karkashin tutatar jam’iyyar PDP, ya sha kaye a zaben 2015 a hannun Muhammadu Buhari na APC.

Kiran wayar da ya yi wa Buhari nan take, inda ya amince da kayen sa kafin a kammala sanar da sakamakon karshe, yasa ya samu yabo saboda ya dakile yiwuwar samun tashin hankali na bayan zabe a kasar.

Bayan barin shi ofis, tsohon shugaban ya zama wani babban dan siyasa na duniya, yana jagorantar muhimman ayyukan sa ido kan zabe da sulhu na lumana a fadin Afirka a madadin Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma (ECOWAS) da Kungiyar Hadin Kan Afirka (AU).

Duk da matsayinsa na dan siyasa babba, hasashe kan yiwuwar dawowar Jonathan cikin fagen siyasa na ci gaba da wanzuwa. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here