2022: JAMB ta bawa dalibai damar fitar da shaidar jarabawar gwaji

JAMB
JAMB

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB) ta umarci dalibai su je su fitar da shaidar jarabawar gwaji ta shekarar 2022.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar ta na mako-mako daga ofishin magatakardar hukumar a ranar Litinin a Abuja.

JAMB ta ce daliban da suka yi rajistar UTME kuma suka nuna sha’awar zana jarabawar za su iya fitar da takardun.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa hukumar ta tsara gudanar da jaabawar ne a ranar 9 ga Afrilu.

JAMB ta ce ana sa ran daliban za su biya Naira 1,000 ga cibiyoyin jarrabawar kwamfuta (CBT) inda za su zana jarrabawar a matsayin kudin hidima.

NAN ta ruwaito cewa JAMB ta tsara gudanar da jarabawar UTME na shekarar 2022 daga ranar 6 ga Mayu zuwa 16 ga Mayu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here