Shugaba Tinubu ya isa Nairobi don halartar taron Afirka

IMG 20260511 WA0001 2 768x589 1 750x430

Shugaba Bola Tinubu ya isa filin jirgin saman kasa da kasa na Jomo Kenyatta dake Nairobi Kenya, da safiyar Litinin domin halartar taron Afirka na (Africa Forward Summit) da zai mayar da hankali kan saka jari da ci gaba mai dorewa a fadin Afirka.

Jirgin Shugaban ya sauka ne da misalin karfe 12:18 na dare agogon yankin, a cewar wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa, Mista Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Litinin a Nairobi.

Tinubu ya gana da Sakataren Majalisar Ministocin Kenya kan Harkokin Waje da Masu Gudun Hijira, Musalia Mudavadi, Jakadan Kenya a Najeriya, Isaac Parashina, manyan jami’an Kenya da mambobin ofishin jakadancin Najeriya a Nairobi.

Taron Afirka da Faransa zai gudana ne a hadin gwiwar Shugaban Kenya William Ruto da Shugaban Faransa Emmanuel Macron, inda ya zai hada shugabannin Afirka, masu tsara manufofi, masu saka jari da ci gaba domin tattauna ci gaba, kirkire-kirkire da hadin gwiwa ta dabarun Nahiyar.

Halartar Tinubu na nuna jajircewar Najeriya wajen cigaba da hadin kan Afirka, karfafa hadin gwiwar tattalin arziki na yanki da habaka haɗdn gwiwa na dabarun da ke da nufin hanzarta ci gaba mai dorewa da habaka ababen more rayuwa a fadin Nahiyar.

Taron zai mayar da hankali kan sauya fasalin tattalin arziki, kirkire-kirkire na dijital, fadada ciniki, ci gaban ababen more rayuwa, sauyin yanayi da dabarun aiki da aka tsara domin inganta wadata tare da ci gaba mai dorewa a fadin Afirka da ma kasashen ketare.

A lokacin taron, ana sa ran Tinubu zai gudanar da tarurruka biyu da bangarori da ban da da ban da nufin karfafa alakar diflomasiyya da tattalin arzikin Najeriya da kasashen Afirka da kuma karfafa jagorancin Najeriya a nahiyar.

Cikin wadanda suke cikin tawagar shugaban akwai Ministan Harkokin Waje, Bianca Ojukwu, Ministan Noma, Sanata Abubakar Kyari, da Ministan Ruwa da Tattalin Arzikin Teku, Adegboyega Oyetola, da sauran jami’ai.

Sauran da ke cikin tawagar sun hada da Ministan Muhalli, Balarabe Lawal, Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dr. Jumoke Oduwole, da Ministan Sadarwa, Kirkire-kirkire da Tattalin Arzikin Dijital, Bosun Tijani.

Ambasada Sola Enikanolaiye, Mrs Omotenioye Majekodunmi, da Jakadan Najeriya a Faransa, Ambasada Ayodele Oke, tare da manyan jami’ai da ke kula da harkokin sauyin yanayi, diflomasiyya da inganta saka hannun jari na daga cikin ‘yan rakiyar shugaban.(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here