JAMB ta sake sakin karin wani sakamakon jarrabawar UTME

JAMB

Hukumar dake shirya jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire (JAMB), ta saki wani sabon sakamakon jarrabawar da dalibai suka rubuta a ranar Litinin, 20 ga watan Afrilu.

Kakakin hukumar ta JAMB, Fabian Benjamin ne ya sanar da sakin sakamakon a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata. Duk da dai bai fadi adadin daliban da aka saki sakamakon na su ba.

Benjamin yace, daliban da suka rubuta jarrabawarsu a ranar Litinin za su yi duba sakamakonsu na jarrabawar, ta hanyar da aka saba.

A ranar Asabar din da ta gabata, hukumar ta JAMB ta saki sakamakon jarrabawar da aka rubuta a ranar Juma’a da Asabar na dalibai 1,264,940.

Tun da fari dai hukumar ta saki sakamakon dalibai 632,752 da suka rubuta jarrabawa a ranar Alhamis, wanda ya kai adadin dalibai 1,897,692 kafin ranar Litinin.

Dalibai da dama sun koka kan jinkirin da aka samu kafin sakin sakamakon jarrabawar da aka rubuta a ranar Juma’a, wanda hakan yasa suka asarar kudade da hukumar ke chaza yayin duba sakamakon.

Hukumar dai ta yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi mata na maida wa daliban kudadensu, inda tace dama bata sanar da sakin sakamakon ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here