Masu ruwa da tsaki a yankin Kano ta Arewa sun nuna goyon bayansu ga Barau, tare da watsi da ta Gwarzo

Barau Barau 1

Masu ruwa da tsaki a yankin Kano ta Arewa sun jaddada goyon bayansu ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, tare kuma da yin watsi da shirin da tsohon karamin ministan gidaje, Abdullahi Tijjani Gwarzo ke yin a neman tsayawa takarar sanatan yankin.

A wata takarda da shugaban kungiyar Kano North Political Stakeholders Forum, Aliyu Abbas Gumawa ya sanyawa hannu a ranar Litinin, masu ruwa da tsakin sun jaddada goyon bayansu ga Sanata Barau.

Kungiyar tace, “mun yi nazari kan yadda siyasar yankinmu take a halin da ake ciki, saboda haka mun tsaida matsayar cewa baza mu goyi bayan burin da Abdullahi Gwarzo ke da shi ba.”

Kungiyar ta kuma nuna damuwarta kan yadda ‘yan takarar neman sanata a yankin kamar su Gwarzo, ke ta nuna sha’awarsu na tsayawa takara, inda ta bayyana hakan da kawo cikas ga ci gaban yankin.

Kungiyar tace ya kamata a bar jama’ar yakin su zabi abin da suke so, a daina tsoma baki a siyasar yankin musamman mutanen da ba ‘yan asalin yankin ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here