Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya taya al’ummar jihar murnar zagayowar Eid-el-Fitr, wanda ke nuna kammala azumin watan Ramadan cikin nasara.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Gwamna Yusuf ya bayyana Eid-el-Fitr a matsayin lokaci na godiya da tunani tare da sabunta kuduri kan darajojin imani da hadin kai da tausayi, kamar yadda aka nuna a duk tsawon watan Ramadan.
Ya bukaci mazauna jihar da su gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana da tsari, yana mai gargadin su guji duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Gwamnan ya jaddada muhimmancin ci gaba da rike juriya da hakuri da girmama juna da zaman tare cikin lumana tsakanin al’umma, ba tare da la’akari da bambance-bambance ba.
Ya kuma bukaci iyaye da masu kula da yara su ba su shawarwari su kasance masu bin doka tare da nuna halaye na gari a lokacin bukukuwan.
Gwamna Yusuf ya kuma karfafa wa jama’a gwiwa su nuna kauna da tallafawa marasa galihu, daidai da koyarwar addinin Musulunci.
Ya sake tabbatar da kudurin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyi, tare da tabbatar da cewa an dauki matakan tsaro da suka dace domin tabbatar da gudanar da bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali a fadin jihar Kano.













































