Gwamnatin Kano ta ba da umarnin yin bincike kan mutuwar matar aure sakamakon zargin sakacin likitoci a Asibiti

Aishatu Umar 540x430

Hukumar kula da asibitocin Jihar Kano ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan mutuwar wata matar aure mai suna Aishatu Umar, bayan iyalanta sun danganta rasuwarta da zargin sakacin likitoci sakamakon tiyatar da aka yi mata a cibiyar kula da masu lalurar fitsari da ke Abubakar Imam a Jihar Kano.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa marigayiya Aishatu Umar, mazauniyar Kano kuma matar aure, ta rasu ne bayan abin da iyalanta suka bayyana a matsayin sakacin likitoci biyo bayan wata tiyata da aka yi mata a asibitin masu fama da lalurar mafitsara na Abubakar Imam.

Iyalin sun bayyana cewa lamarin ya biyo bayan matsaloli da suka taso bayan aikin tiyatar.

A cewar wani rubutu da ɗaya daga cikin ’yan uwanta, Abubakar Mohammed, ya wallafa a shafin sada zumunta, Aishatu wadda take da miji da ’ya’ya biyar, ta rasu ne da tsakar dare bayan ta shafe watanni tana fama da rashin lafiya.

Ya ce an yi mata tiyata a asibitin ƙwararru tun a watan Satumba, amma bayan aikin ta ci gaba da fama da matsanancin ciwon ciki.

Mohammed ya ƙara da cewa marigayiyar ta koma asibitin sau da dama tana kukan halin da take ciki, amma a duk lokacin ana ba ta magungunan rage raɗaɗi ne kawai ba tare da gano ainihin matsalar ba.

Ya bayyana cewa sai kwanaki kaɗan kafin rasuwarta aka gudanar da gwaje-gwaje da hotunan bincike, inda aka gano cewa an bar almakashi a cikin cikinta tun lokacin tiyatar da aka yi mata.

Karanta: Kula da gurɓatar muhalli: Kano ta ƙudiri aniyar ganin masana’antu sun bi  ƙa’ida 100% yayin da tashoshin tace dagwalo ke gab da kammalawa

Ya bayyana cewa ana shirin yi mata wata tiyatar, amma mutuwa ta riga ta riske ta kafin a aiwatar da hakan.

Iyalin sun bayyana lamarin a matsayin sakaci mai tsanani, tare da kira ga hukumomin da abin ya shafa su gudanar da bincike mai zurfi domin tabbatar da adalci ga marigayiyar.

A wata sanarwa da jami’ar hulɗa da jama’a ta Hukumar kula da asibitocin Jihar Kano, Samira Suleiman, ta fitar, ta ce sakataren zartarwa na hukumar, Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya bayar da umarnin fara bincike nan take kan lamarin domin gano gaskiyar abin da ya faru a asibitin Abubakar Imam.

Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar ta jajanta wa iyalan marigayiyar tare da tabbatar da cewa binciken zai kasance a bayyane, ba tare da nuna son kai ba, kuma cikin kwarewa.

Hukumar ta jaddada cewa za a ɗauki matakin da ya dace bisa ƙa’idoji idan aka tabbatar da sakaci, tare da bayyana cewa kare lafiyar marasa lafiya na daga cikin manyan abubuwan da take ba da fifiko a Jihar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here