Tinubu ya sake fasalin kwamitin gudanarwar kula da harkokin wutar lantarki na ƙasa NERC

NERC New 1

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da sake fasalin kwamitin Hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta ƙasa bayan majalisar dattawa ta tantance tare da tabbatar da mambobin kwamitin a ranar Talata.

Wannan mataki ya biyo bayan kammala tsarin tantancewar da majalisar ta gudanar.

Wannan bayani ya fito ne daga wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a birnin Abuja.

Sanarwar ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin ƙarfafa ayyukan hukumar da kuma ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da ake yi a ɓangaren wutar lantarki.

An naɗa Dakta Musiliu Oseni a matsayin shugaban hukumar.

Kuma nadin ya fara aiki a matsayin kwamishina tun watan Janairu na shekarar 2017, daga bisani aka naɗa shi mataimakin shugaban hukumar.

Naɗin nasa a matsayin shugaba ya fara aiki daga ranar ɗaya ga watan Disamba na shekarar 2025, kuma zai ci gaba har zuwa cikar wa’adin aikinsa na shekaru goma kamar yadda dokar wutar lantarki ta shekarar 2023 ta tanada.

Haka kuma an naɗa Dakta Yusuf Ali a matsayin mataimakin shugaban hukumar, kuma an fara naɗa shi a matsayin kwamishina tun watan Fabrairu na shekarar 2022, inda sabon matsayinsa na mataimakin shugaba ya fara aiki daga ranar ɗaya ga watan Disamba na shekarar 2025, kuma zai gudana har zuwa kammala wa’adinsa na farko.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Nathan Shatti da Dafe Akpeneye, waɗanda ke wa’adinsu na biyu bayan an fara naɗa su tun shekarar 2017, da Aisha Kanti Bello wadda ke wa’adinta na biyu bayan shiga hukumar a shekarar 2020.

Haka kuma Chidi Ike yana wa’adinsa na farko bayan naɗa shi a shekarar 2022, yayin da Fouad Animashaun ya shiga wa’adinsa na farko daga watan Disamba na shekarar 2025, inda yake da ƙwarewa a fannin tattalin arzikin makamashi da aikin wutar lantarki a Najeriya.

Shugaban ƙasar ya umurci mambobin kwamitin da su zurfafa tare da ƙarfafa sauye-sauyen da ake aiwatarwa a ɓangaren wutar lantarki, tare da bukatar su su gudanar da ayyukansu bisa doka da ƙa’idar dokar wutar lantarki ta shekarar 2023.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here