Majalisar Dattawa ta shiga yanayi na hayaniya a ranar Alhamis yayin tantance Reno Omokri da aka gabatar a matsayin jakada.
Zaman tantancewar majalisar ya rikice bayan wasu ‘yan majalisa biyu sun shiga munanan muhawara kan ci gaba da amincewa da Reno Omokri.
Damuwa ta fara bayyana lokacin da aka gabatar da shawarar amincewa da Reno Omokri da sauran wadanda ake tantancewa ta hanyar barinsu su tashi su wuce ba tare da tambayoyi ba, sai Sanata Ali Ndume ya dage cewa dole a sami wanda zai mara bayanin kafin a ci gaba.
Sanata Adams Oshiomhole ya ƙi yarda, yana neman a bashi damar yin magana kafin a mara bayanin shawarar.
Ya nuna cewa batun nadin Reno Omokri na da al’amurra masu tayar da hankali a bainar jama’a da ba za a kau da kai daga gare su ba.
Karin labari: Majalisar wakilai za ta binciki zargin kashe masu zanga-zanga da sojoji suka yi a Adamawa
Sanata Ndume ya ci gaba da tsoma baki yana jaddada cewa dokokin majalisar sun buƙaci a mara bayanin shawarar kafin a fara wata tattaunawa, lamarin da ya haifar da hayaniya da musayar maganganu masu zafi tsakanin ‘yan majalisar
Hargitsi ya ƙaru har ya kai ga zage-zage kafin shugaban zaman ya dakatar da hayaniyar ya kuma bukaci a dawo da nutsuwa.
Bayan an samu natsuwa, ba a sami damar yi wa Reno Omokri wata tambaya ba yayin da Sanata Joel Onowakpo Thomas ya mara bayanin shawarar farko.
Majalisar ta amince da shawarar da ta ba da damar Reno Omokri da sauran waɗanda ake tantancewa su tashi su wuce, tare da kammala dukkan zaman ba tare da ƙarin muhawara ba.










































