Rahoton leken asiri ya danganta sace ɗalibai na baya-bayan nan da kisan kwamandan ƴan ta’adda a luguden wutar sojojin sama a Jihar Neja – Wata Majiya

download 6

Sabbin bayanan leken asiri sun nuna cewa sace yaran makaranta da aka yi kwanan nan a wasu yankuna na jihohin Kebbi da Neja na da alaƙa da kisan wani gawurtaccen kwamandan ƴan ta’adda mai suna Babangida, sakamakon luguden wutar rundunar sojin saman Najeriya a Jihar Neja.

Wata Majiyar tsaro mai tushe ta bayyana wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN cewa al’ummomin yankin bakin kogin Shiroro suna murnar tabbatar da mutuwar Babangida, wanda aka dade ana nema tsawon lokaci.

Majiyar ta ce Babangida yana daga cikin manyan na hannun daman shugaban ‘yan ta’adda Dogo Gideh, kuma mutuwarsa ta faru ne ranar 18 ga Nuwamba yayin da ake ba shi magani saboda raunukan da ya samu a harin da sojojin sama suka kai a wajen kauyen Kurebe, inda dama wasu ‘yan ta’adda suka mutu.

Bisa ga bayanan da aka tattara, sace yaran makaranta na iya zama martani daga mabiyan Babangida domin nuna ƙarfi da kuma jaddada tasirin kungiyarsu bayan raunuka da suka sha sakamakon matsin lamba daga ci gaba da hare-haren sojoji.

Karanta: Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da sace ɗalibai, ta zargi makarantar da rashin bin umarnin tsaro 

Rahotanni sun nuna cewa, bayan mutuwar Babangida, shugabannin al’umma daga garuruwa kamar Kwaki, Buresidna, Chukuba, Buwidna, Kuchidna, Banda, Shalupe da wasu yankuna sun ziyarci gidansu a Palleli ranar 19 ga Nuwamba, inda aka tarar da mahaifiyar Gideh cikin damuwa.

Wani babban jami’in leken asiri ya bayyana wannan kisa a matsayin babban koma baya ga kungiyar, sai dai ya yi gargadin cewa mabiyan kungiyar na iya ƙaddamar da karin hare-haren ramuwar gayya da za su iya shafar al’ummomi, makarantun da ke da rauni, da jami’an tsaro.

Ya ce hukumomin tsaro sun karɓi umarnin tsaurara shiri, tare da ƙara kaimi a ayyukan bincike da sintiri domin hana ƙarin hare-hare da kuma ganin an ceto ɗaliban da aka sace.

Mazauna yankin sun nuna farin ciki game da hallaka kwamandan, suna cewa hakan ya basu kwarin gwiwar cewa ayyukan ‘yan ta’adda za su ragu a yankin da abin ya fi shafa.

Hukumomin soja sun tabbatar da cewa za su ci gaba da haɗa kai a ayyukan ƙasa da sama har sai an karya ƙarfin ƙungiyoyin ta’addanci gaba ɗaya a yankin.

NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here