Tinubu ya rantsar da Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar Zabɓe ta ƙasa

Amupitan being sworn in by President Tinubu on Thursday October 23 2025

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rantsar da Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC.

Bikin rantsuwar ya gudana ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, mako guda bayan da majalisar Dattawa ta abbatar da naɗin Amupitan wanda shugab a Tinubu ya aike mata da sunansa a ranar 16 ga watan Oktoba.

Labari mai alaƙa: Yanzu-Yanzu: Majalisar Dattawa ta tabbatar da Farfesa Amupitan a matsayin shugaban hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC)

Shugaba Tinubu ya bukaci Farfesa Amupitan da ya kare martabar Zaɓe a ƙasar nan da kuma tabbatar da bin dokokin hukumar INEC.

Idan za a iya tunawa, naɗin Amupitan ya zo bayan da majalisar Dattawa ta kammala tantace shi da kuma yin nazari kan irin gudunmawar da zai iya baiwa hukumar INEC a yayin jagorancinta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here