Jami’ar Tarayya ta Dutsin-ma da ke Jihar Katsina ta samu tallafin kudaden bincike na Naira miliyan 32 daga gidauniyar bincike ta kasar Afirka ta Kudu.
Mai magana da yawun Jami’ar Malam Habib Umar cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce za a yi amfani da asusun ne wajen bunkasa bincike da hadin ma’abota ilimi a harkar bincike
“NRF wata hukuma ce a Gwamnatin Afirka ta Kudu ta kirkira don ba da gudummawa da cigaban kasa ta hanyar tallafawa da haɓaka bincike ta hanyar kuɗi.
Da yake mayar da jawabi akan tallafin, Shugaban Jami’ar Dutsen-Ma, Farfesa Armaya’u Hamisu-Bichi, ya taya al’ummar jami’ar murnar wannan gagarumin nasara dasukayi.
Hamisu-Bichi ya tabbatar wa cibiyar kudurinsa na cigaba da karfafa ta don samun karin tallafi, don bunkasa karfin ma’aikata da dalibai ga irin wadannan masu bincike.
Ya yabawa Cibiyar Bincike da Ci Gaban Jami’ar bisa kokarin tabbatar da tallafin da kuma sanya sunan jami’ar a idon duniya domin cimma burinta.













































