Yajin aiki: Gwamnatin tarayya ta yi barazanar amfani da dokar “ba aiki, ba biya” ga ƙungiyar ASUU

ASUU vs Federal Government 1

Gwamnatin tarayya ta gargaɗi ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU) da ta guji tafiya yajin aiki, tana mai jaddada cewa dokar “ba aiki, ba biya” tana nan daram kuma za a aiwatar da ita matuƙa.

Ministan ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa, tare da karamin minista mai kula da harkar ilimi, Farfesa Suwaiba Sai’du Ahmad, ne suka bayyana hakan cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai da hulɗa da jama’a na ma’aikatar ilimi ta tarayya, Boriowo Folasade, ya fitar a ranar Lahadi.

A cikin sanarwar, ministocin sun bayyana cewa gwamnati tana da cikakken niyyar ci gaba da tattaunawa da ASUU domin samo mafita mai ɗorewa ga matsalolin da ke addabar tsarin jami’o’i.

Sun ce gwamnati ta nuna gaskiya da haƙuri a tattaunawa da ƙungiyar, inda mafi yawan korafe-korafen ASUU aka riga aka warware su, ciki har da ƙara kaso mai yawa na alawus ɗin koyarwa da inganta yanayin aiki ga malamai.

Ministocin sun kuma jaddada cewa gwamnati za ta tsaya kan bin dokokin ƙwadago da ke akwai, musamman dangane da ladabtar da rashin da’a da tabbatar da gaskiya.

Labari mai alaƙa: Da ɗumi-ɗumi: Ƙungiyar ASUU ta sanar da fara yajin aiki a faɗin ƙasa

A cewar su dokar “ba aiki, ba biya” tana nan bisa tsarin doka, kuma gwamnati za ta yi amfani da ita idan aka katse ayyukan karatu a jami’o’i.

Sanarwar ta ƙara da cewa sauran matsalolin da suka rage suna ƙarƙashin ikon majalisun gudanarwa na jami’o’in da aka sake kafawa kwanan nan domin su kula da irin waɗannan al’amura na cikin gida.

Haka kuma, gwamnati ta bayyana takaicinta kan yadda ASUU ta ci gaba da yajin aiki duk da cewa ta cika dukkan wa’adin da aka cimma a tattaunawa.

Ministocin sun jaddada cewa ƙarƙashin shirin “Sabuwar Fata” na shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu, gwamnati tana ci gaba da bai wa malamai da tsarin jami’o’i muhimmanci, tare da tabbatar da dorewar karatu ba tare da katsewa ba.

Sun bukaci ASUU da sauran ƙungiyoyin ilimi da su rungumi tattaunawa da haɗin kai maimakon rigima, domin cigaban tsarin ilimi da makomar ɗaliban ƙasa.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here