Matatar Dangote za ta fara raba man fetur kyauta daga Litinin, ta rage farashin lita

Refinery CNG Tanker 750x430

Matatar mai ta Dangote za ta fara shirin raba man fetur kyauta daga ranar Litinin mai zuwa.

Mai magana da yawun kamfanin Dangote Group, Anthony Chiejina, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis.

Ya ce shirin zai fara ne a jihohin Kudu maso Yamma, Babban Birnin Tarayya Abuja, Kwara, Delta, Ribas da Edo.

Sanarwar ta ƙara da cewa matatar ta rage farashin man fetur zuwa N841 a kowace lita a Lagos da jihohin Kudu maso Yamma, yayin da a Abuja, Edo, Kwara, Ribas da Delta farashin zai kasance N851 a kowace lita.

Karin labari: Matatar man Dangote ta sake rage Farashin man fetur

An tunatar da cewa shirin rabon man kyauta ya kamata ya fara tun watan Agusta, amma aka samu jinkiri saboda matsalolin sufuri daga kasar China.

Rahotanni sun nuna cewa matatar ta karɓi manyan motocin dakon mai sama da 1,000 domin fara shirin.

A cikin sanarwar ranar Alhamis, kamfanin Dangote ya ce ya kaddamar da shirin amfani da manyan motocin CNG a matakin kasa domin karfafa jigilar kayayyaki da rage farashin rarraba albarkatun man fetur a cikin gida.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here