Za’ayi Jana’izar Buhari A Daura Ranar Talata -Radda

President Buhari 1

QGwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa a yanzu za a yi jana’izar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata 15 ga Yuli, 2025, a mahaifarsa ta Daura.

Allah ya yi wa tsohon shugaban Najeriya rasuwa a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025, a wani asibiti a birnin Landan na kasar Birtaniya.

Gwamna Radda ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Katsina ranar Litinin.

“Tsarin binne mahaifinmu, wanda ya rasu jiya a Landan, mun yi shawarwari da iyalai da mutanen da ke kusa da shi a Landan.

“Mun yanke shawarar cewa gawar zata isa Katsina da rana tsaka kuma za a yi jana’izar a Daura da misalin karfe 2 na rana,” in ji Gwamna Radda.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here