Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta garkokin Addinin Musulunci, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ayyana ranar Asabar 1 ga Maris a matsayin ranar farko ta watan Ramadan.
Sarkin Musulmin wanda ya bayyana hakan ta kafar yada labaran kasar ya ce kwamitin ganin wata na Majalisar Sarkin Musulmi ya samu rahotanni daga sarakunan gargajiya da malaman addini a fadin kasar na ganin jinjirin watan Ramadan.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa Sarkin Musulmi ya bukaci al’ummar Musulmi da su sadaukar da kansu a cikin watan Ramadan
Labari mai alaƙa: An ga watan azumin Ramadan na 2025 a Saudiyya
Ya kuma bukaci al’ummar Musulmi da su yi amfani da lokacin Ramadan wajen yi wa Najeriya da shugabanninta addu’a
Sai dai Sarkin Musulmi ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su zauna lafiya da juna, ya kuma bukaci masu hannu da shuni da su tallafa wa mabukata da marasa galihu domin yin Azumi cikin sauki.
Sarkin ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da ya karawa shugabanni hikimar tafiyar da al’amuran Nijeriya.










































