Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta ce wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe ‘yan sanda 2 tare da yin garkuwa da mutum daya a karamar hukumar Taura.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, faruwar lamarin a Dutse ranar Litinin.
Shiisu ya ce lamarin ya faru ne bayan da ‘yan bindigar suka kai farmaki gidan wani Alhaji Ma’aru Abubakar da ke garin Kawalam suka yi awon gaba da shi.
“A ranar 23/01/2022, da misalin karfe 01:30 na safe, muka samu labarin cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari garin Kwalam da ke karamar hukumar Taura.
“Bayan samun rahoton, mun tura tawagar ‘yan sanda, inda suka nufi wurin da lamarin ya faru. Da muka isa mun tarar ‘yan bindigar sun gudu.
An harbe ASP Anas Usaini da Sunusi Alhassan a kusa da wata motar sintiri da ‘yan bindigar suka kona musu wuta.
“Bincike na farko ya nuna cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan Alhaji Ma’aru Abubakar mai shekaru 60 a garin Kwalam inda suka yi awon gaba da shi,” in ji Shiisu.
Ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da kokarin ganin an kubutar da wanda abin ya shafa, tare da cafke wadanda ake zargi da guduwa.










































