Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ce za ta shiga tattunawa da kungiyoyin kwadago kan batun cire tallafin man fetur a kasar.
Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron kungiyar da aka kammala da sanyin safiyar Alhamis a Abuja.
Fayemi ya ce gwamnonin jihohi 36 sun gana kuma sun tattauna batutuwan da suka shafi kasar da suka hada da cire tallafin da kuma dokar gyara zabe.
“Mun tattauna batun tallafin man fetur kuma muka kammala tattaunawa da shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da kuma kungiyar ‘yan kasuwa.
“Za mu sanar da su kan yadda za a magance wannan matsala ba tare da haifar da wata matsala ba amma da nufin ceto tattalin arzikin Najeriya ga al’ummar Najeriya a karshen wannan rana.
“Don haka, za mu shigar da shugabannin kungiyar NLC a matsayin shugabanni na kasa kuma da nufin tabbatar da cewa sakamakon aikin mu zai kasance cikin tattaunawar kasa,” in ji Fayemi.
Da yake magana kan ko mene ne ra’ayin kungiyar kan farashin Naira 302/lita a matsayin farashin man fetur, Fayemi ya ce lamarin ba wani mataki ne na gwamnonin ba, al’amarin da ke wuyan gwamnatin tarayya ne kadai.
Ya ce duk da cewa wannan nauyi ne da ya rataya a wuyan Majalisar Tattalin Arzikin Kasa, gwamnonin na bayar da tasu gudunmuwar a muhawarar.
Fayemi ya kuma yabawa majalisar dattawan kan yadda ta gaggauta kawar da abubuwan da ke haifar da cece-kuce a cikin daftarin dokar gyaran zabe.
Ya bayyana fatan cewa majalisar wakilai za ta yi koyi da shi, domin a mayar da dokar zaben da aka yi wa kwaskwarima ga shugaban kasa domin amincewa a kan lokaci.
Wannan a cewarsa zai baiwa cibiyoyi daban-daban, musamman hukumar zabe mai zaman kanta damar ci gaba da gudanar da ayyukanta na zabuka daba













































