Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, a ranar Litinin ta tabbatar da zaben gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto.
Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris, Sai’du Umar, ne ya kalubalanci ayyana Aliyu a matsayin zababben gwamnan jihar.












































