Kimanin tsaffin ma’aikatan rukunin tashoshin Vision FM da ke Kano 13 ne suka buƙaci hukumar gudanarwar rukunin tashoshin da ta biya su bashin albashin da suke bin gidan rediyon kimanin naira miliyan 8 da dubu 500.
Cikin wata doguwar wasiƙa ta hannun Lauyan su B. A Muaz, ya buƙaci da a biya tsaffin ma’aikatan bashin da suke bi cikin kwanaki 7, wanda rashin cimma wannan matsaya, za su garzaya da maganar gaban kotu domin ɗaukar matakin sharia.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa kimanin ma’aikatan tashar Vision FM 13 ne suka ajiye aikinsu a watan Mayun wannan shekara ta 2021.
Cikin takaddar ajiye aikin da tsohon manajan tashar Malam Adamu Ladan ya jogaranta ga shugaban rukunin tashoshin Vision na birnin Abuja.
Tsofaffin ma’aikatan sun ce, an ɗauke su aiki ne bisa yarjejeniyar aikin wucin gadi na tsawon watanni 6 kafin ɗaga likkafar su zuwa cikakkun ma’aikata, tun a watan janairun shekarar 2019, wanda har wa’adin watanni shidan ya cika ba a kaiga yi musu komai ba.
Haka kuma sun ce duk da tunatarwar da suke wa hukumar gudanarwar gidan kan bashin da suke bi, amma ba wani tagomashi da aka yi kan wannan lamari.
Cikin wasikar da lauyan tsaffin ma’aikatan ya aike wa manema labarai ciki har da jaridar Solacebase ya nuna sunayen tsaffin ma’aikatan da lamarin ya shafa da suka hada da tsohon manajan tashar Malam Adamu Ladan, Muhammad Garba, Ahmad Rufai Bello, Captain Abdullahi Adamu Bakoji, Saddik Muhammad Kiyawa, Aliyu Abubakar Getso, da Mustapha Khamis.
Sauran ma’aikatan su ne Malam Ashiru Shehu Kachako, Isyaku Turaki Maje, Lami Sumayya Murtala, Samira Adnan, dakuma Lami Shema.
Rahotanni sun nuna cewa, tuni tsaffin ma’aikatan suka aike da kwafin wannan ƙorafi ga babban sifeton ƴan sanda na ƙasa da mataimakinsa na shiyya ta ɗaya da ke Kano da kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano da daraktan hukumar tsaro farin ta DSS da kuma daraktan hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC shiyyar Kano.












































